Ephesians 6

ʼYaʼya da Iyaye

1ʼYaʼya, ku yi biyayya ga iyayenku gama ku na Ubangiji, abin da ya dace ku yi ke nan. 2Doka ta farko wadda aka haɗa da alkawari ita ce: “Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka” 3“don ka zauna lafiya ka kuma yi tsawon rai a duniya.”
M Sh 5.16
4Iyaye, kada ku tsokane ʼyaʼyanku. Ku yi musu reno mai kyau. Ku koyar da su ku kuma gargaɗe su game da Ubangiji.

Bayi da Iyayengiji

5Bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya. Ku nuna musu halin ban girma, kuna kuma yin musu biyayya cikin dukan abu, da zuciya ɗaya kamar ga Kiristi kuke yi. 6Ku yi aiki sosai, ba don kawai ku gamshe su saʼad da suke kallonku ba. Da yake ku bayin Kiristi ne, ku aikata nufin Allah da dukan zuciyarku. 7Ku yi aikinku da kyakkyawar niyya, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba mutane ba. 8Gama kun san cewa Ubangiji zai ba da lada ga kowa gwargwadon kowane aiki nagarin da ya yi, ko shi bawa ne ko ʼyantacce.

9Ku masu bayi, dole ku bi da bayinku da kyau. Ku daina ba su tsoro. Ku tuna, da ku da su Maigida ɗaya kuke da shi a sama, kuma ba ya nuna bambanci.

Kayan Yaƙi na Allah

10A ƙarshe, bari ƙarfin ikon Ubangiji yǎ ba ku ƙarfi. 11Ku yafa dukan kayan yaƙin da Allah yake bayarwa don ku iya kāre kanku daga dabarun Shaiɗan. 12Gama ba da mutane da suke nama da jini muke yaƙi ba. Muna yaƙi ne da ikoki da hukumomi da masu mulkin duhu da kuma a ikokin da suke cikin a sararin sama. 13Saboda haka sai ku yafa dukan kayan yaƙi na Allah, domin saʼad da ranar mugun nan ta zo, ku iya yin tsayin daka, bayan kuma kuka gama kome, ku ɗage. 14Saboda haka fa ku ɗage, gaskiya ta zama ɗamararku, adalci yǎ zama sulkenku, 15shirin kai bisharar salama yǎ zama kamar takalmi a ƙafafunku. 16Ban da waɗannan kuma, ku ɗauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku iya kashe dukan kiban wutar Mugun nan da ita. 17Ku kuma ɗauki ƙwalƙwalin ceto, da takobin Ruhu, wato Maganar Allah, 18a ko yaushe kuna adduʼa da roƙo ta wurin ikon Ruhu ba fāsawa. A kan wannan manufa ku zauna a faɗake da matuƙar naci, kuna yi wa dukan tsarkaka adduʼa. 19Ku kuma yi adduʼa domina, don duk saʼad da na buɗe bakina, in sami kalmomi babu tsoro don in sanar da asirin bishara, 20wadda nake jakadanta cikin sarƙoƙi. Ku yi adduʼa don in iya yin shelarta babu tsoro, yadda ya kamata in yi.

Gaisuwar Ƙarshe

21Tikikus, ƙaunataccen ɗanʼuwa da kuma amintaccen bawa cikin Ubangiji, zai faɗa muku kome, domin ku ma ku san yadda nake da kuma abin da nake yi. 22Na aike shi gare ku musamman don wannan, domin ku san yadda muke, yǎ kuma ƙarfafa ku. 23Salama zuwa ga ʼyanʼuwa, da kuma ƙauna tare da bangaskiya daga Allah Uba da kuma Ubangiji Yesu Kiristi. 24Alheri yǎ tabbata ga dukkan masu ƙaunar Ubangiji Yesu Kiristi da ƙauna marar ƙarewa.

Copyright information for HauSRK